![]() |
|
|
|
Imaninmu Game Da Biyayya Ga ImamaiMun yi imani da cewa Imamai su ne “Ulul’amri” Shugabannin da Allah ya yi umarni a yi musu biyayya, kuma su masu ba da shaida ne a kan mutane, kuma su ne kofofin Allah kuma tafarki zuwa gareshi, masu shiryarwa zuwa gare shi, su ne taskar iliminsa, masu fassara wahayinSa, rukunan TauhidinSa, ma’ajiyar saninSa, don haka suka kasance aminci ga mazauna bayan kasa, kamar yadda taurari suke aminci ga mazauna sama kamar yadda ya zo daga Manzon Allah (S.A.W). A wani hadisin yana fada: “Misalinsu a cikin wannan al’umma tamkar jirgin Annabi Nuhu (AS) ne wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya dakata ya bar shi to ya nutse ya halaka. Kuma ya zo a Kur’ani mai girma “Su sai dai bayin Allah ne ababan girmamawa, ba sa rigonsa da magana, kuma su da umarninsa masu aiki ne”. Surar Anbiya: 26-27. Kuma su ne wadanda Allah ya tafiyar masu da dauda ya tsarkake su tsarkakewa. Mu mun yi imani da cewa umarninsu umarnin Allah ne, haninsu hanin Allah ne, biyayya gare su biyayya ce gare shi, saba musu kuma saba masa ne, kuma Soyayya gare su soyayya ce gare shi, kiyayya gare su kiyayya ce gare Shi, bai halatta ba a mayar musu domin mai mayarwa gare su tamkar mai mayarwa ga Allah ne, kuma ya wajaba a mika wuya gare su da biyayya ga umarninsu, da riko da maganganunsu. Saboda haka mun yi imani da cewa hukunce-hukuncen Shari’ar Ubangiji ba sa samun shayarwa sai daga ruwansu, kuma bai halatta a karbe ta ba sai daga garesu, kuma nauyin da aka dora wa baligi ba ya sauka daga kansa ta hanyar komawa ga waninsu. Kuma mukallafi ba ya samun nutsuwa da cewa ya bayar da wajibin da aka dora masa sai ta hanyarsu. Su kamar jirgin ruwan Annabi Nuhu (A.S) ne duk wanda ya hau ya tsira, wanda kuwa ya jinkirta ya bar su ya dulmuye a cikin wannan ambaliyar da take makale da igiyoyin ruwan rikitarwa, da bata, da da’awoyi, da jayayya. Bahasin imamanci game da tabbatar da cewa su ne halifofi na shari’a kuma masu shugabanci da izinin Allah a wannan zamanin ba shi ne muhimmi ba, wannan al’amari ne na tarihi da ya wuce, kuma tabbatar da shi ba zai sake dewo mana da zamanin da ya wuce na tarihi ba, ko kuma ya dawo musu da hakkinsu da aka kwace na tafi da hukuncin Allah na shari’a ba. Abin da yake muhimmi shi ne abin da muka ambata na wajabcin komawa zuwa garesu wajan karbar hukunce-hukuncen shari’a, da kuma sanin abin da manzo (S.A.W) ya zo da shi kamar yadda ya zo da shi ta fuska ingantacciya. Karbar hukunce-hukunce daga masu ruwaya da kuma Mujtahidan da ba sa sha daga daddadan ruwan mashayarsu, kuma ba sa neman haskakawa daga haskensu, nisanta ne daga tafarkin daidai a Addini. Kuma baligi ba ya taba samun nutsuwar cewa ya sauke nauyin takalifin da ya hau kansa daga Allah, domin tare da samun irin wannan sabanin ra’ayoyi a tsakanin jama’ar musulmi dangane da hukunce-hukuncen shari’a, sabanin da ba a sa ran dacewa a kansa, to fa babu wata dama ga baligi ya zabi mazhabar da ya ga dama ko ra’ayin da ya zaba, dole ne ya yi bincike har ya kai ga hujja tabbatacciya tsakaninsa da Allah (S.W.T) wajen ayyana mazhaba kebantacciya, wacce ya hakikance cewa da ita ce zai isa zuwa ga hukunce-hukuncen Allah, kuma cewa da ita ne zai sauke wa kansa nauyi da aka farlanta, domin abin da ake da yakinin wajabcinsa yana lizimta wajabcin samun yakinin sauke nauyinsa. Dalili tabbatacce da yake nuna wajabcin koma wa Ahlul Baiti (A.S) da kuma cewa su ne ainihin wadanda za a koma gare su a kan hukunce-hukunce bayan Annabi (S.A.W) sun hada da fadinsa (S.A.W): “Hakika Ni na bar muku abin da idan har kuka yi riko da shi ba za ku taba bata ba har abada bayana, Assakalaini, dayansu ya fi dayan girma; su ne littafin Allah igiya mikakkiya daga sama zuwa kasa, da kuma Zuriyata Ahlin gidana, ku saurara ku ji, ku sani cewa su ba masu rabuwa da juna ba ne har su riske ni a tafki”[1]. Ka zurfafa tunaninka game da wannan hadisi mai girma zaka samu abin da zai gamsar da kai ya kuma girgizaka a wannan hadisin a ma’anarsa a fadinsa (S.A.W): “Matukar kun yi riko da su ba zaku taba bata ba a bayana har abada” abin da ya bar mana su ne sakalaini tare, ya kuma sanya su abubuwa guda biyu, bai wadatu da riko da daya ba, ba tare da dayan ba, da riko da su ne ba zamu taba bata ba har abada. Duba kuma ma’anar fadinsa (S.A.W) cewa: “Ba zasu taba rabuwa ba har sai riske ni a tafki” da nunin cewa wanda ya raba tsakaninsu bai yi riko da su a hade ba to ba zai taba samun shiriya ba har abada, don haka ne suka zama su ne; “Jirgin ruwan tsira” kuma “Aminci ga mazauna kasa” da duk wanda ya bar su, to ya nutse a cikin guguwar bata ba kuma zai amintu daga halaka ba, fassarar wannan da ma’anar soyayya gare su ba tare da riko da maganganunsu da bin tafarkinsu ba, gudu ne daga gaskiya da ba abin da yake kaiwa ga hakan sai bakin ra’ayin jahiliyya, da gafala daga tafarki madaidaici a fassarar bayanan zancen Larabci mai fasaha.
[1] Masu ruwaya a tafarkin Sunna da Shi’a sun haxu a kansa.
|