![]() |
|
|
|
Imaninmu Game Da AnnabciMun yi imani da cewa annabci aiki ne na Allah kuma jakadanci ne na ubangiji (S.W.T) da yake bayar da shi ga wanda ya so ya kuma zaba daga bayinsa na gari da masoyansa kammalallu a mutumtakarsu, sai ya aika su zuwa ga sauran mutane domin shiryar da su ga abin da yake da amfani da maslaha garesu duniya da lahira, tare kuma da nufin tsaftace su da tsarkake su daga daudar miyagun dabi’u, da munanan al’adu, da koya musu hikima, da ilimi, da bayyana musu hanyoyin rabauta da alheri, domin ‘yan adamtaka ta kai ga kamalarta da ta dace da ita, ta daukaka zuwa ga daraja madaukakiya a gidajen duniya da lahira. Kuma mun yi Imani cewa ka’idar tausasawa -kamar yadda bayaninta zai zo- ta wajaba ga Allah mahalicci mai ludufi ga bayinsa, ya aiko manzanninsa ne domin su shiryar da dan Adam, da kuma isar da sakon kawo gyara, kuma su zamanto jakadun Allah kuma halifofinSa. Kamar yadda muka yi imani da cewa Allah madaukakin sarki bai ba wa mutane hakkin ayyana Annabi ba ko tsayar da shi -takara- ko zabensa. Ba su da wani zabi a kan haka, domin al’amarin dukkan wannan yana hannun Allah ne, domin “Shi ne mafi sanin inda zai sanya sakonSa”. Surar An’am Aya ta 124. Kuma ba su da wani hukunci a kan wanda Allah zai aiko shi a matsayin mai shiryarwa, mai albishir ko mai gargadi, ko kuma su yi hukunci kan abin da ya zo da shi na daga hukunce-hukunce, da sunnoni, da shari’a. Imaninmu Game Da Cewa Annabci Tausasawa NeMutum halitta ne mai iyakoki mai ban al’ajabi, mai sarkafaffun gabobi a halittarsa, da dabi’arsa, da ruhinsa, da kuma hankalinsa, kai hatta ma a kowane daya daga cikin mutane, dabi’ar fizguwa zuwa ga fasadi sun tattara a cikinsa, kamar yadda dabi’ar motsarwa zuwa ga aikata alheri da gyara suka tattara a cikinsa[, ta wata fuskar kuma an halitta shi a kan halayyar dabi’ar zuciya da dabi’o’i daban-daban kamar son fifita wani a kansa, da sha’awa, kuma an halitta shi a kan son rinjaya da mamayar waninsa, da kwadayin rayuwar dauniya, da adonta, da kawarta, da tarkacenta, kamar yadda Madaukakin sarki yake cewa: “Hakika mutum yana cikin hasara”. Surar Asri: 2. “Hakika mutum yana dagawa. Don kawai ganin ya wadata”. Surar Kalam:6-7. “Hakika rai mai umarni da mummuna ce”. Surar Yusuf: 53. Da sauran ayoyi makamantan wadannan da suke bayyanawa a sarari da nuni ga irin yadda ran mutum yake kunshe da adifa da kuma sha’awa. A wani bangaren, Ubangiji madaukaki ya halitta masa hankali mai shiryarwa da yake shiryar da shi zuwa ga gyara da ayyukan alheri, da kuma zuciya mai gargadi da take hana shi aikata mummuna da zalunci, tare da aibata shi a kan aikata abin da yake mummuna abin zargi. Husumar cikin zuciyarsa da take cikin ran mutum ba ta gushewa tsakanin hanakali da adifa, duk wanda hankalinsa ya yi galaba a kan adifarsa to yana daga cikin mafi kololuwar matsayi masu shiryarwa a ‘yan adamtakarsu, kuma su ne kammalallu a ruhinsu, wandanda kuwa adifarsu ta rinjaye su, to lalle suna daga cikin masu hasarar matsayi, masu cibaya a ‘yan Adamtaka, masu gangarawa zuwa ga matsayin dabbobi. Mafi tsananin abokan gabar rai su ne zuciya da rundunarta, saboda haka ne muke samun mafi yawancin mutane sun dulmuye a cikin bata, suna nesa da shiriya ta hanyar bin sha’awace-sha’awace da amsa kiran zuciya: “Kuma mafi yawan mutane ba zasu zama muminai ba koda kuwa ka yi kwadayin haka”. Surar Yusuf: 103. Saboda gazawar mutum da rashin tsinkayonsa game da abubuwan da suke kewaye da shi, da asiran abubuwan da suke kewaye da shi, da ma wadanda suke bullowa daga cikinsa shi kansa, ba zai iya sanin dukkan abin da zai cutar da shi ko ya amfane shi ba shi da kansa, kuma ba zai iya sanin abin da zai kai shi ga samun sa’ada ko tsiyacewa ba, shin a kan abin da ya kebantu da shi ne shi kadai, ko kuwa wanda ya shafi ‘yan Adam baki daya da kuma al’ummar da take kewaye da shi. Shi bai gushe ba yana jahiltar kansa kuma yana kara jahilci ko kuma kara gane jahilcinsa duk yayin da iliminsa game da halittu na dabi’a da sauran samammu na binciken ilimi ya karu ba. Saboda haka mutum a tsananin bukatarsa ta son kai wa ga darajar sa’ada yana bukatar wanda zai dora shi a kan hanya mikakkiya bayyananniya zuwa ga shiriya, domin rundunar hankali ta karfafa da hakan, kuma ya iya yin galaba a kan abokin gabarsa yayin da ya shiga fagen faman gwabzawa tsakanin rundunar hankali da na zuciya. Saudayawa bukatar wanda zai kama hannunsa zuwa ga alheri da gyara tana kara tsananta ne yayin da zuciya take yaudarar sa ta hanyar nuna masa kyawun fandarewarsa, sai ta nuna masa abin da yake mummuna cewa kyakkyawa ne ko kuma kyakkyawa cewa mummuna ne, ta kuma rikita wa hankali tafarkinsa zuwa ga gyara, da sa’ada, da ni’ima, a lokacin da shi ba shi da masaniyar da zai bambance dukkan abin da yake mai kyau mai amfani da kuma wanda yake mummuna mai cutarwa. Koma kowane mutum ya sani cewa yana cikin wadannan gwagwarmayar dauki-ba-dadi ko ya sani ko bai sani ba sai dai wanda Allah ya kare shi. Saboda haka abu ne mawuyaci ga mutum masanin ilimin zamani ya kai kansa ga dukkan tafarkunan alheri da amfani, da kuma sanin dukkan abin da zai amfane shi ko ya cutar da shi a Duniya da Lahira, ballantana kuma jahili. Al’amarin ya kebance shi ne ko kuma ya shafi al’umma da yake zaune a cikinta ne, kuma ba ya iya kai wa ga wannan masaniyar koda kuwa ya hada kai ya yi taimakekeniya da sauran mutane da ke tare da shi, kuma koda kuwa sun hadu sun yi bincike ko sun yi tarurruka da zama daban-daban da kuma shawarwari. Don haka ne ya zama wajibi Ubangiji ya aiko da Annabawa da Manzanni a cikin mutane domin rahama da tausasawa gare su. “Manzo daga cikinsu yana karanta musu ayoyinSa yana tsarkake su kuma yana koya musu littafi da hikima”. Surar Juma’a: 2. Domin su yi wa mutane gargadi game da abin da yake da cutarwa gare su, da yi musu albishir da abin da yake da alheri, da gyara, da sa’ada, a gare su. Tausasawar Allah ga bayinSa wajibi ce domin tana daga cikin tsantsar kamalarSa, shi mai tausasawa ne ga bayinSa, mai yawan baiwa, mai karimci, idan kuwa har ya zamanto a wani guri da ya dace akwai bukatar ya kwarara kyautarSa da tausasawa, to babu makawa ya kwararo tausasawarSa domin babu rowa a farfajiyar rahamarSa, babu tawaya a kyautarSa da karimcinSa. Ma’anar wajibi a nan ba yana nufin cewa wani zai umarce shi da aikata haka ba, sai ya wajabta a kan Allah madaukakin sarki ya bi shi, Allah ya daukaka ga haka daukaka mai girma! Ma’anar wajibci a nan tana daidai da ma’anar fadinka da kake yi cewa shi wajibin samuwa ne wato ba zai taba yiwuwa a kore masa samuwa ko a raba shi da ita ba. Imaninmu Game Da Mu’ujizar AnnabawaMun yi imani da cewa yayin da Ubangiji (S.W.T) yake sanya wa bayinsa mai shiryarwa ko manzo, to babu makawa ya sanar da shi gare su ya kuma nuna musu shi a ayyane. Wannan kuwa ya takaita ne a kan sanya musu wani dalili da kuma kafa musu hujja a sakon domin cika tausasawarsa da kuma kammala rahamarsa. Kuma wannan dalilin dole ya kasance ya zo daga mahaliccin halittu mai juya al’amuran samammu[, wato ya zama abin da ya gagari kudurar dan Adam, sai ya sanya shi a hannun shi Manzon mai shiryarwa domin a san shi da shi, kuma mai shiryarwa zuwa gare shi, wannan dalili shi ake kira mu’ujiza saboda kasancewarsa ya gagari dan Adam ya gudanar da irinsa, ko kuma ya zo da misalinsa. Kamar yadda babu makawa ga Annabi ya zo da mu’ujiza ya bayyana ta ga mutane domin ya kafa musu hujja, haka nan babu makawa wannan mu’ujizar ya bayyanar da ita ta yadda za ta gagari malamai da kuma kwararrun zamaninsa ballantana sauran mutane, tare kuma da danganta wannan mu’ujizar da da’awar Annabci daga shi mai mu’ujizar saboda ta kasance dalili a kan da’awarsa. Idan irin wadancan kwararru suka gaza zuwa da irinta sai a sani cewa ta fi karfin ikon dan Adam, kuma ta keta al’ada, daga nan sai a san cewa ma’abocinta yana sama da kudurar dan Adam, kuma yana da alaka da mai juya al’amuran samammu. Idan wannan ya tabbata ga mutum -bayyanar mu’ujiza wadda ta saba wa al’ada- ya kuma yi da’awar Annabci da sako, to sai ya zamanto abin gaskatawar mutane ga kiran da yake yi tare da yin imani da sakon nasa da bin maganarsa da umarninsa, sai wanda zai gaskata shi ya yi imani da manzancinsa da kaskan da kai ga umarninsa, wanda zai yi imani da shi ya yi, wanda kuma zai kafirce masa ya kafirce. Wannan shi ne abin da ya sa muka ga cewa mu’ujizar kowane Annabi ta dace da abin da ya shahara a zamaninsa na ilimi da fasaha, mu’ujizar Annabi Musa ita ce sanda wanda take hadiye sihiri da abin da suke yin baduhunsa saboda kacancewar sihiri a zamaninsa shi ne fannin fasaha da yake mashahuri, yayin da sandan ya zo sai dukan abin da suke aikatawa ya baci, suka san cewa wannan abu ya fi karfinsu, kuma yana saman fannin fasaharsu, kuma dan Adam ya gajiya ya kawo shi, kuma kwarewa da ilimi sun gajiya a gabansa . Hakanan mu’ujizar Annabi Isa (A.S) ita ce warkar da makafi da masu baras, da raya matattu, saboda shi ya zo ne a lokacin da likitanci ne yake ya yadu a tsakanin mutane, kuma akwai malamai likitoci da suke da kwarewa mai girma, sai iliminsu ya kasa gogayya da abin da Isa (A.S) ya zo da shi. Mu’ujizar Annabinmu madawwamiya ita ce Kur’ani mai girma mai gajiyarwa -ga waninsa na daga fasahohi- da balagarsa da fasaharsa a lokacin da balagar magana ta kasance ita ce fanni sananne, ma’abota ilimin balaga da azancin magana su ne kan gaba a tsakanin mutane da kyawun bayaninsu da daukakar fasaharsu, sai Kur’ani ya zo musu kamar tsawa, ya dimautar da su, ya fahimtar da su cewa su ba zasu iya fito na fito da shi ba. Don haka suka sallama masa rinjayayyu bayan sun gaza gasa da shi, suka ma gaza isa ga kurar da ya tile su da ita ya wuce ya barsu . Ya kuma kalubalance su da su kawo sura goma suka kasa, yayin da muka ga sun gajiya sai muka ga sun koma fada da shi da takobi maimakon harshe, sai muka san cewa lallai Kur’ani wani abu ne na mu’jiza da ya zo daga Muhammad dan Abdullahi hade da da’awar manzanci, sai muka san cewa ya zo ne da gaskiya kuma ya gasgata shi. Imaninmu Game Da Ismar AnnabawaKuma mun yi imani da cewa Annabawa ma’asumai ne dukkaninsu, haka nan Imamai (A.S), sai dai mun saba da wasu daga cikin musulmi a kan haka don su ba su wajabta isma ga Annabawa ballantana ga Imamai (A.S). Isma: lta ce tsarkaka daga aikata zunubi da sabo kananansu da manyansu da kuma kubuta da tsarkaka daga mantuwa koda kuwa hankali bai kore aukuwar haka daga Annabi ba, kuma wajibi ne ya tsarkaka hatta daga dukkan abin da yake zubar da mutunci kamar cin abu a kwararo a tsakanin mutane, ko kuma kyalkyala dariya da sauti mai girma, da dukkan aikin da ake munana yin sa a tsakanin mutane. Dalilin da ya sa Isma ta zama wajibi shi ne: Da ya halatta ga Annabi ya aikata sabo, ko kuma ya yi kuskure, ko ya yi mantuwa, kuma kuma wani abu makamancin wannan ya auku daga gare shi, da sai ya zamanto imma dai ya wajaba a yi masa biyayya a aikin da ya yi na sabo ko kuskure, ko kuwa bai wajaba ba, idan har ya wajaba to da mun halatta aikata sabo da dogaro da rangwame daga Allah, kai mun wajabta ne ma, wannan kuwa abu ne batacce na larurin Addini da na hankali, idan kuwa biyayya gare shi ba ta wajaba ba a kan haka, to kuwa wannan ya kore Annabcin da babu makawa tana tare da wajabcin biyayya har abada. Ta kowane hali dai aiki ko zance ya zo daga gareshi da ya zama muna tunanin sabo ne ko kuskure, sai ya zama ba wajibi ba ne a bi shi a cikin kowane abu, sai fa’idar aiko Annabawa ta zamanto ta tafi haka nan, sai Annabin ya zama kamar sauran mutane da maganarsa ba ta da wata kimar da za a dogara a kanta da’iman, kamar yadda biyayya gare shi ba za ta zama tilas ba, babu kuma nutsuwar zuciya da maganganunsa da ayyukansa baki daya. Wannan kuwa dalili ne a kan cewa Isma tana tare da Imami, domin kaddarawar cewa shi zababbe ne daga Allah (S.W.T) don shiryar da bayi a matsayin halifan Annabi, kamar yadda zamu yi karin bayani a fasalin Imamanci. Imaninmu Game da Siffofin AnnabiMun yi imani da cewa, kamar yadda ya wa.jaba Annabi ya zamanto ma`asumi, haka nan ya wajaba ya zamanto mai siffantuwa da mafi kamalar siffofin dabi’a da hankali wadanda mafifitan su, su ne jarumtaka, da iya tafiyar da al’amuran mutane, da shugabanci, da hakuri, da karfin kwakwalwa da hazikanci, har ya zamanto babu wani daga cikin mutane da zai yi kusa da shi a kan haka, domin ba don haka ba, da bai inganta ba ya zamanto yana da shugabanci a kan dukkan halittu baki daya ba, ko ya zamanto yana da karfin tafiyar da al’amuran duniya dukkaninta ba. Haka nan wajibi ne ya zamanto mai tsarkin haihuwa dan halas, amintacce, mai gaskiya, wanda yake tsarkakakke daga dukkan miyagun dabi’u kafin aiko shi saboda zukata su nutsu da shi, rayuka kuma su karkata zuwa gareshi, kuma domin ya cancanci wannan matsayi mai girma daga Ubangiji. Imaninmu Game Da Annabawa Da LittattafansuMun yi imani a dunkule da cewa dukan Annabawa da Manzanni a kan gaskiya suke, kamar yadda muka yi imani da ismarsu da tsarkinsu, musanta Annabcinsu kuwa da zaginsu da isgili da su yana daga kafirci da zindikanci, domin yin haka yana nufin karyata Annabinmu wanda ya ba da labari game da su da kuma gaskiyarsu. Wadanda aka san sunayens da shari’o’insu kamar Annabi Adam (A.S) da Annabi Nuhu (A.S) da Annabi Ibrahim (A.S) da Annabi Dawud (A.S) da Annabi Sulaiman (A.S) da Annabi Musa (A.S) da Annabi Isa (A.S) da sauran Annabawan da Alkur’ani ya ambace su a sarari ya wajaba a yi imani da su a ayyane, duk kuwa wanda ya karyata daya daga cikinsu to ya karyata su baki daya kuma Ya karyata Annabcin annabinmu a kebance. Haka nan ya wajaba a yi Imani da littattafansu da abin da aka saukar musu. Amma Attaura da Injila da suke hannayen wadanda aka canzasu daga yadda suka sauka saboda abin da ya auku gare su na daga canje-canje da sauye-sauye, na daga kari da ragi bayan zamanin Annabi Musa da Annabi Isa (A.S) saboda wasan da ma’abuta son rai da kwadayi suka yi da su, wadanda ake da su yanzu mafi yawancinsu ko ma dukkansu kagagge ne da ya aka farar a zamanin mabiyansu bayan wucewarsu (A.S). |