![]() |
|
|
|
Abin da Muka Yi Imani Da Shi Game Da Mahadi (A.S)Hakika albishir da bayyanar imam Mahadi (A.S) daga ‘ya’yan Fadima (A.S) a karshen zamani domin ya cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci ya tabbata daga Annabi (S.A.W) ta ruwayoyi masu yawa, kuma dukkan musulmi duk da sabanin mazahabobinsu sun ruwaito hadisai game da shi. Fikirar samuwar imam mahadi (A.S) ba wani sabon abu ba ne da Shi’a suka kago shi saboda iza su da yaduwar zalunci ya yi zuwa gare shi, har suka yi mafarkin bayyanar wani wanda zai zo ya tsarkake kasa daga daudar zalunci, kamar yadda wasu masu neman kawo rikici da rudani marasa adalci suka raya. Ba don tabbatar akidar Mahadi (A.S) daga Annabi (S.A.W) ba, ta yadda dukkan musulmi suka san ta kuma ta kafu a zukatansu suka yi imani da ita, da masu da’awar mahadiyyanci a karnonin farko kamar kaisaniyya, da Abbasawa, da wasu daga Alawiyyawa, da sauransu, ba su iya yaudarar mutane ba ta hanyar samun dama da amfani da wannan akida wajen neman mulki da shugabaci, domin sun sanya da’awar mahadiyyancinsu ta karya ta zama hanyar tasiri a kan jama’a gaba daya da kuma shiga rayukan jama’a. Mu tare da Imaninmu da ingancin Addinin musulunci, kuma cewa shi ne cikamakon addinan Ubangiji, kuma ba ma sauraron wani Addini da zai zo domin gyara dan Adam, hada da abin da muke gani na yaduwar zalunci da yawaitar fasadi a duniya, ta yadda ba zaka iya samun masakar tsinke ba ga adalci da gyara a kasashen duniya, tare da kuma abin da muke gani a fili na nesantar musulmi daga addininsu, da kuma ajiye hukunce-hukuncen musulunci da dokokinsa a gefe guda a dukkan kasashen musulmi, da kuma rashin lizimtuwarsu da koda daya daga dubban hukunce-hukuncensa, amma duk da haka ba makawa mu saurari budi da farin ciki da dawowar Addinin musulunci da karfinsa da iyawarsa wajan gyara wannan duniyar da ta dulmiya cikin takurawar zalunci da fasadi. Sannan kuma ba zai yiwu ba musulunci ya dawo da karfinsa da jagorancinsa a kan dan Adam baki daya ba, alhalin yana kan wannan halin da yake ciki a yau da gabanin yau na daga sabanin mabiyansa a dokokinsa da hukunce-hukuncensa da ra’ayoyinsa game da shi, tare da wannan hali da suka samu kansu a ciki a yau da ma kafin yau na bidi’o’i da canje-canje a dokokinsa, da bata a cikin da’awoyinsu. Na’am ba zai yiwu ba Addini ya koma ga karfinsa sai dai idan mai gyara babba ya jagorance shi, yana hada kansu, yana kuma rushe abin da aka raba masa na daga bidi’o’i da bata, tare da taimakon Ubangiji da ya sanya shi shiryayye mai shiryarwa, wanda yake da matsayi mai girma na Shugabanci na gaba daya, da kuma iko mai sabawa al’ada, domin ya cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci. A takaice; Dabi’ar yanayin fasadi a duniyar dan Adam ta kai matuka a baci da kuma zalunci, duk da kuwa imani da ingancin wannan addini da cewa shi ne cikamakon addinai, wannan al’amari ya hukumta sauraron mai wannan gyara domin tseratar da duniya daga abin da take ciki. Saboda haka ne dukkan bangarorin musulmi suka yi imani da wannan sauraron, kai har da ma wadanda ba musulmi ba, sai dai kawai bambancin da yake tsakanin mazhabar Imamiyya da waninta shi ne, ita mazhabar imamiyya ta yi imani cewa wannan mai gyaran mutum ne ayyananne wanda aka haife shi a shekarar hijira ta 256, kuma bai gushe ba yana raye, kuma shi dan imam Hasan Askari ne mai suna “Muhammad” (A.S). Wannan kuwa saboda abin da ya tabbata daga Annabi (S.A.W) da kuma imamai (A.S) game da alkawarin zuwansa, da haihuwarsa, da boyuwarsa. Bai halatta ba Imamanci ya yanke a wani zamani daga zamuna koda kuwa Imami ya kasance boyayye ne, domin ya bayyana a ranar da Allah ya yi alkawari, wanda kuma wannan yana daga cikin asiran Ubangiji da babu wanda ya san su sai shi. Kuma rayuwarsa da wanzuwarsa ba komai ba ne sai mu’ujiza ce da Allah ya sanya domin ba ta fi mu’ujizar kasancewarsa imami ga mutane yana dan shekara biyar ba a ranar da mahaifinsa ya koma zuwa ga Ubangiji Madaukaki, kuma ba ta fi Mu’ujizar Annabi Isa (A.S) girma ba da ya yi magana da mutane yana cikin shimfida yana jariri, kuma aka aike shi Annabi ga mutane. Tsawon rayuwa fiye da dabi’a fannin likitanci bai musanta shi ba, kuma ba ya ganinsa mustahili, sai dai shi likitanci bai kai matsayin da zai iya kara tsawon rayuwar mutum ba. Idan kuwa likitanci ya gajiya a kan haka to Allah mai iko ne a kan komai. Kuma tsawaita rayuwar Annabi Nuhu (AS) da wanzuwar Annabi Isa (AS) ya faru kamar yadda Kur’ani ya bayar da labari, idan kuwa mai shakka ya yi shakku game da abin da Kur’ani ya ba da Iabari game da shi, to sun yi hannun riga da Musulunci. Yana daga abin mamaki musulmi ya tsaya yana tambaya game da yiwuwar haka alhalin yana da’awar imani da Littafi Mabuwayi. Daga cikin abin da ya zama dole mu ambace shi a nan shi ne cewa; sauraron ba yana nufin musulmi su nade hannayensu game da al’amuran da suka shafi Addininsu ba ne, da kuma abin da ya wajaba na taimakonsa, da jihadi a tafarkinsa, da riko da hunkunce-hukuncensa, da yin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna. Musulmi har abada abin kallafawa ne da aiki da abin da ya sauka na daga hukunce-hukuncen Shari’a, kuma ya wajaba a kansa ya yi kokarin sanin su ta fuska ingantacciya, kuma wajibi ne a kansa ya yi umarni da kyakkyawa, kuma ya yi hani da mummuna gwargwadon daidai yadda zai iya “Dukkanku makiyaya ne kuma kowannenku abin tambaya ne game da abin kiwonsa.” Saboda haka bai halatta gareshi ba ya takaita wajibansa don yana jiran mai kawo gyara Imam Mahadi (A.S), wanda yake mai shiryarwa da aka yi albishir da shi, domin wannan ba ya saryar da takalifin da aka kallafa, ba ya jinkirta aiki, ba ya sa mutane su zama karazube kamar dabbobi. |