Hikimar Imani Da Mai Tseratarwa | ||
|
Ba kokwanto cewa duk wani juyi a duniya yana dauke da wata fikira da yake son isarwa da yadawa, amma fikirar juyin imam Mahadi (A.S) zata kasance musulunci ne, wannan fikira zata zama sanadiyyar rushewar zalunci ta hanyar nuna adalci da yanayin walwalar jin dadin al’umma da ake hankoron kaiwa gareshi. [continue...] | |
Haduwa Da Imam Mahadi (A.S) | ||
|
Bayan share fagen zuwan alamomin bayyanar wannan juyin mai girma a karshen zamani, da zai kasance ta hannun imam Mahadi dan Hasan Askari (A.S) da umarnin Allah. Kamar yadda ya zo a kura’ani mai girma shi ne ragowar na Allah[1] kuma an zabe shi bisa sunnar Allah ta zaben bayinsa na gari. [continue...] | |
Bayyanar Imam Mahadi (A.S) | ||
|
Ruwayoyin Shi'a da Sunna[1] sun zo game juyin imam Mahadi (A.S) wanda zai zo bayan cikar mukaddimominsa da shiryawar duniya don karbarsa, wanda zai fara daga Makka. Kuma za a yi bishara da shi ta hanyar sauti mai tsawa daga sama da safe kamar yadda ya zo a wasu ruwayoyi, da kuma tsawa ta biyu daga yamma bayan faduwar rana ko kuma ranar da take biyo wa bayan taron ma’abota bata da barna. [continue...] | |
Alamomin bayyanar imam Mahadi (A.S) | ||
|
Ta yiwu muna iya cewa al’amarin bayyanar imam Mahadi (A.S) a mahangar Shi'a wani abu ne da Allah ya boye shi kuma ya zama sirri domin samun nasarar imam Mahadi (A.S) a kan makiyansa, don haka ne ma ruwayoyi suka zo suna karyata duk wani wanda yake ayyana lokaci; kamar wata ko shekara ko ranar da zai bayyana. [continue...] | |